Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabban taron kasa: APC ta fitar da tsarin shugabancin shiya-shiyya

Babban taron kasa: APC ta fitar da tsarin shugabancin shiya-shiyya

Date:

Kwamitin riko na jam’iyyar APC a ranar Laraba, ya fitar da tsarin shiyya-shiyya na babban taron kasa da za a gudanar ranar 26 ga Maris.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Salisu Na’inna Dambatta, ya fitar, ta ce jam’iyyar ta mayar da shugaban jam’iyyar na kasa zuwa yankin Arewa ta Tsakiya yayin da yankin Kudu maso Yamma za ta samar da sakataren kasa.

Ya ce ofishin mataimakin shugaban jam’iyyar ya tafi shiyyar Kudu maso Gabas.

Sanarwar ta ce, an amince da tsarin shiyya-shiyya ne a babban  taron kwamitin na ranar 8 ga Maris, 2022.

Sanarwar ta kara da cewa, wakilan kwamitin riko na jam’iyyar na ko wace shiyya ne za su gudanar da aikin tantancewa da kuma fito da yan takarar.

Ga cikakken jadawalin:
KUDU MASO KUDU: Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta, Edo da jihar Rivers

1. Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Kudu maso Kudu )

2. Sakataren yada labarai na kasa

3. Shugabar mata ta kasa

4. Mataimakin ma’aji na kasa

5. Mataimakin Sakataren walwala na kasa

sai kuma sauran mukamai wanda ko wace shiyya tana da nata.

KUDU MASO YAMMA: Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da kuma jihar Oyo

1. Babban Sakatare na kasa

2. Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Kudu maso yamma)

3. Shugaban Matasa na kasa

4. Shugaban masu bukata ta musaman na kasa

5. Mataimakin mai binciken kudi na kasa

sai kuma sauran mukamai wanda ko wace shiyya tana da nata.

AREWA MASO GABAS: Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba sai Yobe

1. Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (shiyar arewa)

2. Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Arewa maso gabas)

3. Mataimakin Sakataren kudi na kasa

4. Mataimakiyar shugabar mata ta kasa

5. Mai binciken kudi na kasa

sai kuma sauran mukamai wanda ko wace shiyya tana da nata.

AREWA MASO YAMMA: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara

1. Mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (arewa maso yamma)

2. Mai bada shawara kan shari’a na kasa

3. Sakataren tsare-tsare na kasa

4. Sakataren kudi na kasa

5. Mataimakin shugaban matasa na kasa

sai kuma sauran mukamai wanda ko wace shiyya tana da nata.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...