Saurari premier Radio
27.4 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuni ba zai sake zama shugaban APC ba-El-Rufai

Buni ba zai sake zama shugaban APC ba-El-Rufai

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnanjihar Yobe, Mai Mala Buni, ba zai iya ƙara zama shugaban jam’iyyar APC ba, a cewar Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i.

Idan za a iya tunawa ranar Litinin din da ta gabata ne Gwamnan Kebbi, Sani Bello ya shiga ofishin jam’iyyar APC na ƙasa a matsayin sabon shugaba.

Gwamna El-Rufa’i ya ce Mai Mala Buni zai dai iya sake zama Gwamnan Yobe, amma ba shugaban APC ba.

Ya ce Gwamna Sani yana da goyon bayan Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da gwamnoni 19.

“Buni ya tafi kenan, sakataren ma ya tafi kenan. A yanzu Gwamna Bello shi ne shugaba kuma yana da goyon bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 19. Buni zai iya sake iya zama Gwamnan Yobe amma ba shugaban jam’iyyarmu ba.

“Shugaba Buhari ne ya bada umarnin a kawar da shi kuma tuni an yi haka. Gwamna Bello ya ɗauki ragamar komai kuma abubuwa suna ci gaba da tafiya daidai. Za a dawo da jam’iyya, za a yi babban taron jam’iyya kamar yadda aka tsara.

“Gwamnoni 19 da mataimakansu suna goyon bayan haka. Buni da mutanensa sun samu umarnin kotu na hana babban taron ƙasa amma sai ya ɓoye”, in ji El-Rufa’i.

Latest stories

Related stories