Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbinda yasa bamu amince da dokar kananan yara ba-Cidari

Abinda yasa bamu amince da dokar kananan yara ba-Cidari

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

Majalissar dokoki ta jihar Kano ta ce taki amincewa da dokar baiwa kananan yara ‘yanci ne la’akari da  yadda wasu sassanta suka ci karo da addinin musulunci da kuma al’adar al’ummar jihar Kano.

Shugaban majalisar Injiya Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana haka yayin hira ta musamman da Premier Radio ranar Laraba.

Chidari, ya ce sun binciki dokar kuma sun dauki matakin gayyatar malamai da masana don ganin anyiwa dokar gyara ta yadda ba za ta ci karo da shari’ar musulunci ko al’adar jama’ar jihar Kano ba.

Ya kuma ce akwai dokar da ke gaban majalisar wacce ake nazarta akan sha da bataucin miyagun kwayoyi.

Dangane da batun cin gashin kan majalisun jihohi da ake danbarwa akai kuwa ya ce tuni jihar Kano taci kaso casa’in cikin dari na baiwa majalisar ikon cin gashin kanta kamar yadda wasu jihohin suka fara a kasar nan.

Ya ce akwai fahimtar juna sosai tsakanin majalisar dokoki ta jihar Kano da ta zartaswa wanda hakan yasa suke zaune lafiya.

Chidari, ya kara da cewa son rai ne zaisa wani yace majalisar dokoki ta jihar Kano bata aiki.

Ya ce akwai aikace aikace da yawa da majalisar dokoki ta jihar Kano ke yi wadanda al’umma basu sani ba.

Ya kara da cewa bawai kawai yin rikici ko tsige gwamna shine aikin ‘yan majalisa ba kamar yadda wasu ke tsammani.

Ya kara da cewa majalisar dokoki ta jihar Kano ta banbanta da sauran majalisun dokoki na jihohi dake kasar nan duba da irin aikace aikacen da takeyi.

Acewarsa majalisar na daga cikin majalisu kalilan a kasar nan dake baiwa al’umma damar bayyana ra’ayin su akan kasafin kudi da gwamnati keyi duk shekara.

Ya kuma ce majalisa tana da kwamiti dake duba yadda ake Tarawa da kashe kudaden gwamnati wanda yake bin diddigi akan duk wani abu da ya shafi kudi.

Latest stories

Related stories