Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWazirin Katsina ya yi murabus

Wazirin Katsina ya yi murabus

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wazirin Katsina Alhaji Abubakar Lugga ya ajiye rawaninsa bayan wata yar tankiya tsakaninsa da Masarautar Katsina.

Mai magana da yawun Masarautar Katsina, Mallam Iro Bindawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Alhamis.

Lugga dai shi ne Wazirin Katsina na 5 da ya fito daga gidan sarautar sullibawa.M

Wata jarida daga jihar Kantsin wato Katsina City News ta ce hakan na zuwa ne a sakamakon takaddamar da ta biyo bayan wani jawabi da Wazirin ya gabatar a Ilorin, babban Jihar Kwara a kan matsalar tsaro da kasar nan ke ciki baki daya.

Bayanai sun ce a wani taron manema labarai da ya gudana a birnin na Ilorin inda aka yi masa tambayoyi a kan yanayin tsaro da Jihar Katsina ke ciki kuma Alhaji Lugga ya ba da bayanin kusan duk abin da manyan Katsina kan furta.

Wannan jawabin nasa, wanda wasu jaridun kasar nan suka dauka a ranar Litinin da ta gabata, ya harzuka masarautar Katsina, lamarin da ya sanya ta rubuta masa takardar tuhuma don neman ya ba da bayani a kan dalilin furucin da ya yi.

 

A bayanin nasa da ya rubuta, Alhaji Sani Lugga ya ba da hujjojinsa na cewa akwai matsalar tsaro a Katsina har ta shafi Kananan Hukumomi takwas da hujjarsa ta cewa an rufe makarantu kuma wasu Hakimai har sun yi kaura daga masarautunsu.

A ranar Alhamis Wazirin na Katsina ya ba da amsa cikakkiya mai shafuka hudu da kwararran hujjoji har da maganganun Gwamnan Katsina, Sarkin Katsina da Sakataren Gwamnatin Jihar.

Kazalika, Alhaji Lugga ya aika wa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa.

A wasikar da ya rubuta mai shafuka biyu, ya kawo tarihin sarautar gidansu ta Kanem Bakashe da ke kasar Nijar, wadda ta samo asali tun 1579.

Kazalika ya kawo tarihin sarautar Waziri a gidansu, wadda ta fara tun 1906. Ya kuma ba da bayanin yadda aka nada shi Wazirin Katsina a 2002, wanda ya ce a yau Alhamis, 24 ga watan Fabrairun 2022 ya ajiye.

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...