Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMuhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani dangane da sabuwar dokar...

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani dangane da sabuwar dokar zabe

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Da safiyar ranar Juma’a ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Dokar Zabe da aka yi wa kwaskwarima, don a inganta harkokin zabe a Najeriya.

Dokar dai gyara ce a kan ta 2010, wacce tun a shekarar 2015 Shugaban ya ki rattaba mata hannu saboda dalilai daban-daban.

Hakan dai ya sa masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin cewa jan kafar da Shugaban ya yi na iya sa ya kammala mulkinsa ba tare da ya bar abin da za a rika tunawa da shi ba.

’Yan Najeriya da dama dai na ta tambayar me zai faru bayan Shugaban ya rattaba hannu a kan dokar.

Ga wasu abubuwa 10 da ya kamata ku sani a sabuwar dokar:

1- Sakar wa INEC kudade a kan lokaci

Sashe na 3 (3) na dokar ya bukaci a gaggauta fitar da dukkan kudaden da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) take bukata don yin zabe akalla shekara daya kafin lokacin gudanar da babban zabe.

Hakan dai ana ganin zai taimaka wa hukumar matuka wajen shirya wa zabukan yadda ya kamata.

2-Yin amfani da na’ura wajen aikewa da sakamakon zabe

A cewar sashe na 50 na dokar, INEC ce ke da alhakin yanke hukuncin ko za a aike da sakamakon zabe ta na’ura mai kwakwalwa ko kuma a’a.

3-Damar sake duba sakamakon zabe in aka tilasta wa jami’an INEC ayyana shi

Sashe na 65 na sabuwar dokar ya ba INEC ikon sake nazartar sakamakon zaben da aka tilasta wa jami’anta suka ayyana shi ta karfin tuwo.

Ana ganin matakin dai zai magance yadda wasu ’yan siyasa kan tilasta wa ma’aikatan INEC su ayyana wanda ba shi ya lashe zaben ba, ta yadda a baya kotu ce kawai za ta iya sake duba shi.

4-Babu ruwan ma’aikatan INEC da shiga jam’iyyun siyasa

Sashe na takwas (5) na dokar ya ce dole ne ma’aikatan INEC su nisanci shiga kowace irin jam’iyyar siyasa.

Hakan dai ya hana duk mamban wata jam’iyya zama ma’aikacin INEC.

Dokar ta kuma ce duk ma’aikacin INEC din da aka samu da alaka da wata jam’iyya ya aikata laifin da zai iya jawo masa tarar Naira miliyan biyar, ko daurin shekara biyu, ko kuma duka biyun.

5-Tantance masu zabe da na’ura

Sashe na 47 na sabuwar dokar har ila yau ya tanadi yin amfani da na’urar Smart Card Reader ko wata na’urar da INEC za ta amince da ita wajen tantance masu kada kuri’a.

6-Tanadi ga masu bukata ta musamman

Kazalika, sashen na 54 (2) na dokar ya tanadi cewa dole ne INEC ta tabbatar ta samar da na’urori na musamman ga masu bukata ta musamman domin su kada kuri’a daidai bukatarsu.

7-Kada kuri’a fiye da kima

Ana samun kada kuri’a fiye da kima ne idan adadin mutanen da suka kada kuri’a suka haura wadanda aka tantance a rumfar zabe.

Sashe na 51 na sabuwar dokar dai ya shardanta cewa daga yanzu adadin mutanen da aka tantance shi ne zai zama hanyar tantance sahihancin zabe.

8-Gudanar da zaben fid da gwani da mika sunayen ’yan takara a kan lokaci

La’akari da tanadin sashe na 29 (1) na dokar, dole ne kowacce jam’iyya ta mika wa INEC sunayen ’yan takararta kwana 180 (wata shida) kafin lokacin zabe, wadanda aka tantance bayan lashe halastaccen zaben fid da gwani.

9-Fara yakin neman zabe wata uku kafin zabe

Sashe na 94 na dokar ya ce an tsawaita lokacin yakin neman zaben ’yan takara da jam’iyyu daga kwana 90 kafin zabe zuwa kwana 150 kafin zabe, kuma za a dakatar da yakin ne sa’a 24 kafin ranar zaben.

10-Canza dan takara idan ya mutu yayin zabe

Sashe na 34 na dokar ya ba jam’iyyu damar sake gudanar da zaben fid da gwani domin canza dan takarar da ya mutu ana tsaka da zabe amma ba a kammala ba, ballantana a ayyana wanda ya yi nasara.

Idan kuwa zaben dan majalisa ne, za a sake shirya zaben a zagaye na biyu, kuma jam’iyyar da dan takarar nata ya rasu za ta samu damar sake shirya zaben fid da gwani cikin kwana 14 don zabar sabon dan takara.

Dangane da zaben Shugaban Kasa da na Gwamna kuwa, Mataimakin dan takarar ne zai maye gurbinsa sannan shi kuma ya zabi mataimakinsa daga bisani.

Latest stories

Related stories