Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIna fatan ganin ranar da zan zama tsohon shugaban kasa-Buhari

Ina fatan ganin ranar da zan zama tsohon shugaban kasa-Buhari

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce yana fatan ganin ranar da zai zama tsohon shugaban kasa bayan ya kammala wa’adinsa na biyu.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar da ya kai wa Sarkin Lafia Mai Martaba Justice Sidi Bage Muhammad na daya mai ritaya a fadarsa.

Buhari na ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Nasarawa, inda ya je don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule ta yi.

“Bisa tsarin da doka ta tanada, ba zan iya zarce wa’adi biyu ba, kuma na yi rantsuwa da Al Qur’ani Mai Girma cewa, zan bi kundin tsarin mulkin Najeriya.” Buhari ya ce kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar a ranar Alhamis ta ce.

“A duk lokacin da aka sa muka rantse da Al Qur’ani Mai Girma, ya zama dole mu yi matukar taka-tsan-tsan. Ya kuma zama dole mu ga cewa ba mu ci amanar jagoranci da Allah ya dora mana ba.”

“Na ga akwai tsoffin gwamnoni a nan, ni ma kuma ina fatan ganin ranar da zan zama tsohon shugaban kasa.” Buhari ya kara da cewa.

Lokaci na karshe da Buhari ya kai ziyara jihar ta Nasarawa shi ne a shekarar 2019.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...