Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin Ukraine da Rasha: Mene ne ya jawo fadan?

Rikicin Ukraine da Rasha: Mene ne ya jawo fadan?

Date:

Rikicin da ya barke tsakanin Ukraine da Rasha ya kai kololuwa cikin ‘yan shekarun nan, ya yinda yunkurin diflomsiyyar da ake yi na taimakawa wajen samo mafita ke samun tasgaro.

Akwai tarin batutuwan da suka haifar da rikicin wadanda an shafe gomman shekaru kuma sun shafi kasashen yankin.

Ya rikicin ya samo asali?

Tun watan Oktobar 2021 wannan matsalar ta fara kunno kai. Shi ne lokacin da Rasha ta fara tura dubban dakarunta zuwa kan iyakarta da Ukraine.

Hotunan tauraron dan Adam da bayanan sirri sun bayyana cewa fiye da sojoji 100,000 ne aka jibge a yankin.

Akwai manyan makamai kamar tankokin yaki da motoci masu sulke da kuma bindgogin da ke iya harbo tankoki da jiragen sama da aka jibge a kan iyakar kasashen biyu.

Ukraine ta bayyana damuwarta game da tara sojojin Rasha a kan iyakarta, sai dai gwamnatin kasar ta ce babu alamar Rasha na daf da kai mata hari a yanzu.

Rasha ma ta ce tara sojojinta a yankin ba ta yi shi bane domin razana Ukraine, kuma ta ce tana da ikon tura sojojinta zuwa inda ta ga dama a cikin kasarta.

Wasu cikin manyan makaman da Rasha ta tura kan iyakarta da Ukraine sun hada da rokoki samfurin S-400 masu iya harbo jiragen yaki

Amma damuwar da wasu ke bayyanawa ita ce kan yadda Rasha ke cewa Nato na son shigar da Ukraine cikin kungiyar ne domin ta sami kafar fada wa Rasha idan damar yin haka ta samu.

Shin da gaske Nato za ta shigar da Ukraine cikin kungiyar?

Ban da rikicin sojin, akwai kuma takardamar diflomasiyya tsakanin Rasha da kungiyar Nato.

Rasha ba ta amince da Nato ta fadada kungiyar ba, kuma tana son a tabbatar mata cewa ba za a bar Ukraine ta shiga kungiyar ba har abada. Wannan matsaya ce da kawarta China ma ke goyon baya.

A halin yanzu Nato na da mambobi 30, sai dai ana iya shigar da wasu kasashen cikin kungiyar.

A shekarun 1990, bayan da yakin cacar baki ya zo karshe da kuma rugujewar tsohuwar Tarayyar Soviet, Nato ta rika neman kulla kawance da sababbin kasashen da suka samu ‘yancinsu a yankin tsakiya da gabashin Turai.

Ukraine ba ta cikin mambobin Nato, sai dai ‘kawa ce’

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Ukraine na iya zama barazana a gare ta idan ta shiga kungiyar ta Nato.

Amma sakatare-janar na Nato Jens Stoltenberg ya ce Rasha ba ta da “wata damar amincewa ko hana wata kasa shiga kungiyar.”

Yayin da ake kokarin diflomasiyya domin magance rikicin, an fara neman wata hanyar ta daban da Ukraine za ta iya amfani da ita domin tabbatar da dangantakarta da Nato.

Ko Rasha na iya afka wa Ukraine?

Kamar yadda ta dade tana furtawa rasha ta ce ba ta da niyyar yin haka, sai dai wasu kalaman nata na rikitar da tunani.

“Ai tuni suka kawo hari,” inji Lutsevych. Yana magana ne kan kwace yankin kudancin Crimea da Rashar ta yi a 2014.

“Fiye da mutum 14,000 sun rasa rayukansu kuma an raunata mutum fiye da 33,000. An dade al’ummar Ukraine na shan bakar wahala karkashin harin da Rasha ke kai mana.”

A watan Janairu sojojin kasar Ukraine sun halarci wani bikin tunawa da sojojin da aka kashe yayin da suke kare kasar.

Nato bata shiga cikin wannan rikicin ba kai tsaye, sai dai ta tura kari sojojinta zuwa kasashen gabashin Turai a karo na farko, cikinsu akwai Estonia da Latvia da Lithuania da Poland da kuma Romania.

Rasha na son a janye wadannan sojojin daga cikin kasashen da muka lissafa a sama.

Sai dai Nato ta ce ba ta da niyyar janye sojojin nata a halin yanzu.

Ko mene ne matakin da Nato za ta dauka yanzu?

Ranar 17 ga watan Fabrairu, Shugaban Jamus Olaf Scholz ya shaida wa Shugaba Joe Biden na Rasha cewa kasarsa na tare da Amurka kan batun kakaba wa Rasha takunkumi da zarar ta kai wa Ukraine hari.

Cikin takunkuman da Amurka ke son kakaba wa Rasha akwai na hana bankuna na kasar amfani da tsarin cinikayya na SWIFT wanda ake aikawa da kudi tsakanin kasashen duniya.

Sai dai har yanzu Nato ba ta ce za ta yi amfani da karfin soja domin mayar da martani kan Rasha ba.

Kuma duk da kokarin da ake yi na sasanta kasashen, har yanzu babu wata hanyar da kasashen za su bi domin cimma wata yarjejeniya.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...