Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Tuesday, April 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRasha ta kaddamar da yaki akan Ukraine

Rasha ta kaddamar da yaki akan Ukraine

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da fara yaki da kasar Ukraine bayan share tsawon makwanni ana zaman tankiya da kuma gazawar matakai na diflomasiyya tsakanin Rasha da kasashen Yammacin Duniya.

Shugaba Putin ya sanar da kaddamar da farmakin yayin  wani jawabin bazata da ya gabatar a gidan talibiji da misalin karfe 6 na safiyar yau agogon Rasha, inda ya bukaci dakarun Ukraine su gaggauta ajiye makamansu musamman a yankunan da ke gabashin kasar ta Ukirane.

Putin, ya ce ya dauki wannan mataki ne domin kauce wa faruwar kisan kiyashin da mahukuntan birnin Kiev suka tsara aiwatarwa a yankin tare da kawo karshen take-take irin na tsokana da kasashe mambobi a kungiyar NATO ke yi wa Rasha.

Ministan tsaron kasar ta Ukraine Dmytro Kouleba ya ce Rasha ta tsara gagarumin shirin mamaye kasar, kuma tun a sanyin safiyar yau ta fara kai hare-hare da kuma jin karar fashewar abubuwa a wasu biranen kasar ciki har da birnin Kiev. Tuni dai Ukraine ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga jiragen da ke jigilar fasinja,

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci tsagaita wuta a cikin gaggauwa, sai kuma shugaba Joe Biden na Amurka wanda ya yi tir da wannan farmaki da Rasha tayin akan Ukraine

Latest stories

Related stories