24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBabu maboyar 'yan bindiga kusa da shalkwatarnu-'Yan Sanda

Babu maboyar ‘yan bindiga kusa da shalkwatarnu-‘Yan Sanda

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhatar Yahya Usman

Rundunar yan sandan kasar nan ta musanta rade-radin da ke yawo cewa an gano wata maboyar ’yan bindiga kusa da shalkwatarta da ke Abuja.

Kakakin ’yansandan Abuja, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Ya ce bidiyon da ake yadawa na karya ne, inda ya shawarci mazauna yankin birnin tarayya kada su firgita.

Ya kara da cewa, an gano wani wurin garkuwa da mutane amma ba a kusa da shalkwatar ba ne.

A don hakan ne ma ya ce bidiyon da ake yadawa makircin makiya ne domin ci gaba da haifar da fargaba a tsakanin mazauna Abuja da al’ummar kasa baki-daya.

Ya kuma ce har yanzu ’yan sanda na ci gaba da kai hare-hare, da lalata gidaje da ka iya zama maboyar masu aikata laifuka a Abuja.

Latest stories