Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliyar ruwa na ci gaba da rusa gidaje a Kano

Ambaliyar ruwa na ci gaba da rusa gidaje a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Ambaliyar ruwa ta rusa gidaje masu yawa a ƙauyuka da dama a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da Ajingi a nan Kano.

Mamakon ruwan sama da ake samu kwanakin nan a jere a jere ne ya yi sanadiyyar ambaliyar tare da rushewar gidajen.

A yankin ƙaramar hukumar Ajingi an sami asarar rayuka tare da asarar dukiyoyi masu yawa.

Haka zalika ginin wata makaranata ya faɗa wa wasu ƴan makaranta wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaya daga cikinsu.

Yankuna da dama a Kano dama wasu jihohi a arewacin kasar nan na fuskantar ambaliyar ruwa, saboda mamakon ruwan sama da ake fuskanta a damunar bana.

A makon da ya gabata ma an shafe kwana uku a jere ana tafka ruwan sama, babu ƙaƙƙautawa, wanda hakan ya shafi harkokin kasuwanci da matsugunan al’umma.

A kauyen Shuwawa da ke yankin Danbagina a Dawakin Kudu, da dama daga cikin mazauna ƙauyen sun bar gida, inda suka tura iyalansu gidajen iyayensu.

Latest stories

Related stories