24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeAl'aduBurtaniya za ta mayarwa da Najeriya wasu kayan tarihinta da ta sa...

Burtaniya za ta mayarwa da Najeriya wasu kayan tarihinta da ta sa ce

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Wani gidan ajiye kayan tarihi a birnin Landan ya amince zai mayar wa Najeriya kayayyakin da aka sata daga ƙasar a ƙarni na 19 daga Masarautar Benin.

Gidan kayan tarihi na Horniman Museum ya ce zai miƙa kayan 72 ga gwamnatin Najeriya.

Kayayyakin sun ƙunshi tagullar Benin 12, da kuma makullin shiga fadar sarki.

Hukumar kula da wuraren ajiye kayan tarihi ta Najeriya ce ta miƙa buƙatar mayar mata kayayyakin a cikin watan Janairu.

Gidan tarihin da ke kudancin Landan ya ce ya shawarci mazauna unguwar da masu ziyara da yara ‘yan makaranta da malaman jami’a da ƙwararru kan al’adu da masu zane-zane da ke Burtaniya da Najeriya kafin ɗaukar matakin.

“Dukkanin korafin da suka gabatar kan makomar Benin mun gamsu, da kuma bukatar al’umma,” a cewar gidan tarihin.

Shugaban gidan tarihin ya ce hakan shi ne mafi “dacewa da da’a” mayar da kayayyakin.

Latest stories