Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnan Kaduna bashi da hurumin korar malaman KASU -ASUU

Gwamnan Kaduna bashi da hurumin korar malaman KASU -ASUU

Date:

Hafsat Bello Bahara

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta kalubalanci gwamna Nasir El-rufa’I ya fito ya nuna ayyukan da yayiwa jami’ar Kaduna KASU da zai bashi hurumin yiwa yayan kungiyar su barazanar kora.

Wannan jawabin ya biyo bayan taron karfafa gwiwwa da shugabancin kungiyar ASUU reshan jihar Kano ya kai jami’ar a yau.

Kwamaret Abdulkadir Muhammad yayin tattaunawarsa da premier radio ya bayyana cewar gwamna El rufa’I bashi da hurumin da zai kori malaman jami’ar ta Kaduna domin su ba malaman firamare bane da zai tashi dare daya yace ya kore su.

Abdulkadir Muhammad ya kara da cewar malaman jami’ar ta KASU sun tabbatar da cewar suna nan daram a cikin kungiyar ASUU kuma zasu cigaba da yajin aiki babu gudu ba ja da baya

A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa’I yaci alwashin korar dukkan malaman jami’ar jihar matukar basu janye daga yajin aikin da kungiyar ASUU ta tsundumaba kusan watanni bakwai da suka gabata.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories