31.9 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiGwamnatin Kano zata kafa Kotun sulhu a tsakanin al'umma a jihar nan.

Gwamnatin Kano zata kafa Kotun sulhu a tsakanin al’umma a jihar nan.

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin Kano zata kafa Kotun sulhu a jihar nan.

 

Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa kotun sulhu a jihar nan.

 

Majalisar ta amince da kafa kotun sulhun ne a zamanta na Larabar nan.

 

Majalisar dokokin Kano za tayi bincike akan Kano Pillars

Cikin ayyukan da kotun sulhun zata rinka gabatarwa sun hada da sasanta al’umma da yin sulhu kan sabanin da suke samu a tsakanin su tare da samar da masalaha kan wasu kanan laifuka.

 

Kotun sulhun dai ta kunshi alkalin alkalai na jihar Kano da girandi kadi da malamai da kuma wakilcin masarautar Kano.

 

Majalisa ta tadakatar da gina shaguna a jikin asibitin Zana a nan Kano

 

A wani labarin

 

Gyaran dokar masu bukata ta musamman ta shekarar 2022 ta tsallake karatu na farko a gaban majalisar dokoki ta jihar Kano.

 

Majalisar ta amince da karatun farko na gyaran dokar ne a zamanta na Larabar nan.

 

Yayin zaman majalisar ta kuma amince da karatun farko na kudirin sauyawa jami’ar kimiya da fasaha ta Wudil suna zuwa Aliko Dangote.

 

‘Yan majalisar dokokin Kano 10 sun sauya sheka daga PDP zuwa NNPP

A ranar Talatar data gabata ne dai majalisar ta karanta wasikar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, dake neman amincewa da sauyawa jami’ar ta garin Wudil suna zuwa Aliko Dangote.

 

A wani labarin

 

Gyaran dokar hukumar kula da magunguna da kayayyaki itama ta tsallake karatu na farko a gaban majalisar.

 

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da nada Justice Ibrahim Umar mai ritaya da Barista Jamila Sani Garko, a matsayin mambobi a hukumar shari’a ta jihar Kano.

 

Majalisar ta amince da nadin nasu ne a zamanta na Larabar nan bayan tantance su da tayi.

 

Idan za a iya tunawa dai a zaman majalisar na ranar Talata ne ta karanta wasikar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya aike mata don tantance mutanen biyu.

 

Inda majalisar ta baiwa kwamitinta na shari’a wanda dan majalisa mai wakiltar Bichi, Lawan Shehu, ke jagoranta don tantance su tare da gabatar da rahotonsa a Larabar nan.

 

‘Iyalan fasinjojin jirgin kasan da aka sace na zanga-zanga a Abuja.

 

Bayan gabatar da rahoton ne kuma a yau Laraba majalisar ta amince da nada su a matsayin mambobi a hukumar shari’ar ta jihar Kano.

Latest stories