Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Tuesday, May 21, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniNFCA reshen Kano ta taya Abdu Maikaba murnan zama sabon kocin Kano...

NFCA reshen Kano ta taya Abdu Maikaba murnan zama sabon kocin Kano Pillars

Date:

Kungiyar Masu horarwa ta kasa reshan jahar Kano ( NFCA) ta taya daya daga cikin mamba a kungiyar Abdullahi Maikaba murnar zama sabon mai horar da Kano Pillars.

Kungiyar wadda Ibrahim Gwadabe (Minta) ke zama Shugaban ta, ya aike da sakon taya murnan ga Abdu Maikaba wanda Mai magana da yawun Kungiyar Jabir Hassan ya fitar kuma aka rabawa manema Labarai.

Sanarwar ta ce Nadine Abdu Maikaba ya zo ne a lokacin da kowa ke kallon nadin nasa ya cancanta da ya jagoranci kungiyar ta Sai Masu Gida.

A ranar Litinin ne dai Mataimakin gwamnan jihar Kano Comrd Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jagoranci gabatar da Abdu Maikaba Fagge a matsayin sabon Mai horar da Kano Pillars.

Aminu Abdussalam wanda ya kasance bako namusamman, ya jagoranci bikin gabatar Abdu Maikaba ne a dakin taro na mataimakin Gwamnan taron da ya samu halartar mutane da dama.

Aminu Abdussalam ya ce dama kungiyar ta Sai Masu Gida a baya rashin jagoranci mai kyau ne ya sanya ta samu wannan koma bayan, wanda ya ke fata a yanzu Abdu Maikaba zai farfado da martabar kungiyar.

Ya kuma ce Gwamnatin Kano a shirye take wajen baiwa harkokin wasanni goyan baya, wanda hakan zai farfado da yadda fannin na wasanni ya gamu da cikas a baya.

Har ma ya kara da cewa tuni shiri ya yi nisa wajen yiwa Filin wasa na Sani Abacha da ma sauran filayen wasanni a Kano garanbawul domin ciyar da harkokin wasanni gaba.

Abdu Maikaba Fagge wanda a baya ya jagoranci kungiyoyi irinsu Enyimba da Akwa United da Wikki Tourist har ma da Enugu Rangers, ya ce zai yi duk Mai yiwuwa domin ganin ya dawo da martabar Kano Pillars.

Ya kuma ce dama Kano gida ce a wajensa, a don haka ma yake da shiri namusamman wanda zai bawa marada kunya wajen ganin ya dawo da kimar Kano Pillars.

Latest stories

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data ƙirƙiri sabbin masarautu gyara.

Majalisar dokokin Kano zata yiwa dokar data kirkiri masarautun...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...