Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniKano Pillars ta sallami masu horarwar da kwantaraginsu ya kare

Kano Pillars ta sallami masu horarwar da kwantaraginsu ya kare

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sallami dukanin Wanda kwantaraginsu ya kare a Kungiyar bayan kammala kakar wasanni ta shekarar 2022/2023.

Shugaban hukumar gudanarwar Kano Pillars Alhaji Babangida Umar Little ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana yawun Kano Pillars Lurwan Idris Malikawa.

Malikawa a zantawarsa da Ahmad Hamisu Gwale ya ce tin daga kan masu Horarwa da yan wasan da kwantaraginsu ya kare duka an sallame su a kungiyar.

Malikawa ya kara da cewa wanda ya samu sakon kira ne kawai zai dawo kungiyar domin tinkarar kaka mai zuwa.

Lurwan Idris Malikawa ya kuma ce kungiyar ta dage dawowa daukar horo data sanya tinda fari na ranar 17 ga wata zuwa ranar Lahadi 23 ga Yuli, har ma Sanarwar ta bukaci duk mai son sake aiki da Kano Pillars to zai iya mika takardunsa ga Kungiyar ta sai masu gida.

Kano Pillars dai ta samu damar dawowa gasar NPFL a kakar wasanni mai zuwa, bayan da ta kammala a mataki ta biyu a wasannin share fage da aka gudanar a Jihar Delta.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories