Saurari premier Radio
28.8 C
Kano
Wednesday, May 1, 2024
Saurari Premier Radio
HomeFIFAAbu uku da ya kamata ku sani a gasar Champions League ta...

Abu uku da ya kamata ku sani a gasar Champions League ta 2023/2024

Date:

Tuni a wannan rana ta Talata 19 ga Satumbar 2023 za a dawo ci gaba da wasannin gasar cin kofin zakarun turai mai cike da dumbin tarihi.

Gasar wadda aka kirkira a shekarar 1955 wato sheakru 68 da suka gabata da farawa, sai dai a shekarar 1992 anyiwa gasar kwaskwarima da har yanzu ake ci gaba da bugawa.

A bana kungiyoyi 32 ne za su fafata gasar mai rukunai sama da guda Takwas daga rukuni na A zuwa rukuni na H.

Wasannin mako na farko na matakin rukunin dai zasu fara gudana daga Talata 19 da Laraba 20 ga Satumba.

Inda kuma za a kammala wasannin rukunin a ranakun 12 da 13 ga watan Disamar shekarar 2023 da muke ciki.

Abu na farko da ya kamata ku sani.

A karo na farko bayan sama da shekara 15 za a buga gasar cin kofin zakarun turai ba tare da manyan yan wasannin duniya Ronaldo da kuma Messi ba.

Messi da Ronaldo
                             Messi da Ronaldo

Wannan na zuwa ne bayan da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka bar Turai da Ronaldo ya koma Saudiyya Messi kuma ya koma Amerika.

Ronaldo shine na farko da ya koma taka leda a gasar Saudi Arabia inda ya ke bugawa kungiyar Al Nassr.

Abokin hamayyarsa kuwa Lionel Messi Inter Miami da ke Amurka.

Kawo yanzu ma akwai sauran fitattun ‘yan wasan da a bana ba zasu buga Champions League sun hada da Neymar da ya koma Al Hilal da Karim Benzema, wanda ya koma Al-Ittihad.

Abu na biyu kuwa shi ne

Manchester City za ta kare Champions League da ta ci a karon farko a tarihin kungiyar da ke kasar Ingila.

City wadda ke karkashin jagorancin Pep Guardiola na rukuni na uku da zata buga da RB Leipzig da Red Star Belgrade da kuma Young Boys.

Dama dai Manchester City kofin Champion League daya ta taba lashewa a tarihin kafa shekaru masu yawa da suka gabata.

Real Madrid ce wadda tafi lashe wannan gasa da Jumulla 14 a tarihi, kuma babu wata kungiya da ta yi shirn kamota.

Abu na Uku shi ne

Alhassan Yusuf
             Alhassan Yusuf

Dan asalin jihar Kano da ke wasa a kungiyar Royal Antwerp Alhassan Yusuf za buga gasar UEFA Champions League a karon farko a tarihi..

Jaridar Independent Mirror ta rawaito cewa Alhassan Yusuf shi ne dan jihar Kano na farko da zai buga wannan gasa wadda aka fara shekara 68 da suka wuce …

Mai Shekara 22 a kakar data gabata ya buga wasa 34 Kuma ya taimaka an zura kwallo biyu a duka wasan da ya buga a kungiyar

Yusuf ya bugawa kungiyoyi irinsu IFK Göteborg da Allsvenskan Kuma Yanzu haka kwantaraginsa da Antwerp zai kaishi har zuwa Yunin,2025.

Alhassan Yusuf ana saran zai fuskanci kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da suke rukuni na H Mai Barcelona, FC Porto da Shakhtar Donetsk.

To amma a ina za a buga wasan karshe a bana?

Ana saran Filin wasa na Wembley da ke kasar Ingila ne zai karbi bakuncin wasan na karshe.

Sai dai kuma akwai batun canja fasalin wasannin Champions League?

Wannan ce kakar karshe daga ita za a sauya fasalin wasannin –

Da hakan ke zama wannan shekarar ce ta karshe da Kungiyoyi 32 zasu kece ranini.

Wato gasar da ake raba rukuni takaws dauke da kungiyoyi hur-hudu kowanne.

Inda biyun da suka ja ragamar rukuni su kai zagaye na Kungiyoyi 16 daga nan Kuma akai zuwa matakin dab dana kusa da karshe.

Kana matakin kusa da karshe daga nan kuma zuwa wasan karshe wato Final.

Yanzu haka dai daga kakar wasannin Shekarar 2024/2025 kungiyoyi 36 ne za su kece raini a tsakaninsu a UEFA Champions League din.

Latest stories

Nan da mako biyu za a fara jigilar maniyyatan jihar Kebbi.

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji...

David Cameron ya ce an gabatarwa kungiyar Hamas tayin tsagaita wuta.

A halin da ake ciki kuma, sakataren harkokin wajen...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...