Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniZargin shigar magoya baya fili ya sanya anci tarar Pillars Miliyan Daya

Zargin shigar magoya baya fili ya sanya anci tarar Pillars Miliyan Daya

Date:

Mahukuntan shirya gasar Firimiyar Najeriya, sunci tarar kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars Naira Miliyan Daya, bayan kammala wasan mako na 4 da Rivers United. 

Hukumar shirya gasar ta (NPFL) ta sanar da daukar wanann matakin ne a ranar Litinin, bayan kwamitin da ya kula da wasan ya mika rahotan sa.

An dai zargi magoya bayan Kano Pillars Da Shiga filin wasa, lokacin da kungiyar ta zura kwallo daya tilo a minti na 93 wasan da aka buga filin wasa na Sani Abacha Stadium.

To sai jim bayan kammala binceken rahotan yadda wasan ya gudana, hukumar ta NPFL tace ta dauki matakin bisa karya dokar B13.18 da magoya bayan Pillars din su kayi.

Tuni ma dai aka umarci kungiyar da ta biya wannan kudi kasa da kwanaki 14, Ko ma rashin biyan kudin kan Lokaci ya sanya hukumar daukar matakin da ya fi wannan.

A gefe guda kuma hukumar NPFL ta gargadi magoya bayan kungiyar Heartland, duk da suma irin laifi makamancin wanda magoya bayan Pillars din su ka aikata.

Magoya bayan Heartland dai sunki barin jamian da zasu jagoranci wasan shiga filin wasa wanda su kai ta hargitsi.

Amma duk da haka, hukumar ta NPFL bata dauki wani mataki mai tsauri a kansu su ba, sai dai gargadin magoya bayan Heartland din kawai da tayi kan abin da suka aikata a wasan mako na hudu da suka buga a karshen mako.

Latest stories

Related stories

NPFL: Kungiyoyi Hudu da suka tsallaka gasar Firimiyar Najeriya

NPFL: Kungiyoyi Hudu da suka tsallaka gasar Firimiyar Najeriya An...