Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniRonaldo ya bukaci Alkalin wasa ya soke Fenality da ya bashi bayan...

Ronaldo ya bukaci Alkalin wasa ya soke Fenality da ya bashi bayan ya gano akwai kuskure

Date:

Dan wasa Cristiano Ronaldo, ya bukaci Alkalin wasa ya soke bugun daga kai sai mai tsaran raga da ya bashi, bayan da ya gano akwai kuskure.

Al-Nassr da Persepolis sun tashi wasa babu ci, a wasan gasar cin kofin Asian Champions League da suka buga a ranar Litinin.

Mai shekara 38 Ronaldo ya ra bauta da bugun daga kai sai mai tsaran raga da Alkalin wasa dan kasar Shina Ma Ning ya ba Shi,sai dai daga baya ya bukaci Alkalin wasan ya soke.

Jim kadan da faruwar hakan, sai aka duba na’urar da ke taimakawa Alkalin wasa VAR kuma ta tabbatar babu Fenality din.

Dama dai Al-Nassr ta kai zagayen kungiyoyi 16 a gasar, tin ma kafin tayi wasan na ranar Litinin a birnin Riyadh.

Kawo yanzu kungiyar da ke buga gasar Saudi Pro League, tana mataki na farko da maki 13 a rukunin na E a wasa biyar, kuma ta bai wa kungiyar da ke mara mata baya tazarar maki biyar.

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...