Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan wasan Kano Pillars na Para-Soccer zasu buga wasan karshe da FCT

Yan wasan Kano Pillars na Para-Soccer zasu buga wasan karshe da FCT

Date:

Daga Ahmad Hamisu Gwale

Yan wasan kwallon guragu na Kano Pillars, sun kai wasan karshe a gasar Para-Soccoer bayan doke yan wasan Plateau da ci 3-2 a yammacin ranar Litinin a ci gaba da buga gasar cin kofin masu bukata tamusamman ta kasa.

Wakilinmu Ahmad Hamisu Gwale ya bamu rahotan gasar na ci gaba da gudana a filin wasa na Moshood Abioloa dake birnin Tarayya Abuja.

Tin da fari yan wasan birnin Tarayya Abuja sun yi nasarar doke yan wasan Kaduna da ci 1-0 da hakan ya basu damar kaiwa wasa karshe a gasar.

Yanzu haka yan wasan Kano Pillars na fara Para-Soccer zasu kece raini da yan wasan birnin Tarayya a wasan da zai gudana a Wannan Talatar.

Gasar cin kofin masu bukata tamusamman ta kasa ta Wannan shekarar ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa ce ke daukar nauyin shiryawa masu bukata tamusamman domin suji ana damawa da su a harkokin wasanni.

Akalla wasanni 15 daban-daban ne ake ci gaba fafatawa a gasar cin kofin masu bukata tamusamman ta kasa dake gudana filin wasa na Moshood Abioloa dake birnin Tarayya Abuja.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...