Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJihar Kano ta samu lambar Zinare ta farko a gasar Para Games...

Jihar Kano ta samu lambar Zinare ta farko a gasar Para Games ta 2023

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

Dan wasa Adeleke Abajoye Odunaya, ya jagoranci jihar Kano fara lashe Lambar Zinare ta farko a bangaren wasan ninkaya na gudun mita 500 a wasan gasar masu bukata tamusamman ta kasa da ke gudana a birnin Tarayya Abuja.

Gasar wasannin masu bukata tamusamman ta kasa karo na biyu, na gudana a filin kasa da kasa na Moshood Abiola dake birnin Tarayya Abuja.

Nasarar lashe Lambar Zinare da dan wasa Adeleke Abajoye Odunaya, ya sanya zai jagoranci Yan wasan jihar Kano bangaren ninkaya domin ci gaba da samun lambobin yabo a gasar da a Yau Litinin aka shiga rana ta Uku ana fafatawa.

Tin a yammacin ranar Lahadi ma Yan wasan Kano na Para-Soccer sun lallasa yan wasan jihar Lagos da ci 9-1 a wasa na biyu da ya gudana.

A wani ci gaban ma yan wasan Kano bangaren wasan Amputee sunyi nasara da ci 4-0 a kan jihar Kaduna, haka ma yan wasan Kano a wasa zagaye na biyu sunyi nasara kan Sokoto da ci 5-1.

Latest stories

Related stories