Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn kama jami'an yan sanda biyu bisa zargin karbar rashawa a hannun...

An kama jami’an yan sanda biyu bisa zargin karbar rashawa a hannun Baturiya

Date:

Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta sanar da kama wasu jami’anta biyu kan zargin karbar rashawa daga wata Baturiya.

Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta dai ya nuna yadda wata baturiya ta nadi bidiyon yan sandan a babur dinta suna tambayarta cin hanci.

Baturiya wadda ta ce ta taho tun daga kasar Netherlands a kan babur za ta je birnin tarayya Abuja.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Iseyin zuwa Ogbomosho da ke Jihar Oyo.
A cikin bidiyon, an ji ‘yan sandan suna tambayar Baturiyar me ta kawo musu bayan haka kuma aka ji suna rokonta kudi.
Sai dai a sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sandan na kasa Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce cewa an kama ‘yan sandan ne saboda halayyar da suka nuna ta rashin kwarewar aiki.

Adejobi ya kuma tabbatar da cewa tuni kwamishinan ‘yan sandan na Jihar Oyo Adebola Ayinde Hamzat ya tanadi tsarin ladabtarwa kan lamarin ba tare da bata lokaci ba.

Alumma dai na ganin halayyar da yan sandan suka nuna tamkar kunyata rudunar ne da kuma zubar da darajar Najeriya a Idon wannan baturiya.

Latest stories

Related stories