Mayakan gwagwarmayar Hamas sun gwabza da sojojin mamaya na Isra’ila a tsakiyar babban birnin Gaza inda Isra’ila ke kyautata zaton akwai babban jagoran Hamas, da hakan ya sa Isra’ilan ta matsa ƙaimi tare da yiwa yankin ƙawanya.

Shaidu sun ce sojojin Isra’ila cikin manyan motoci da tankunan yaƙi masu sulke sun yi ta kai-kawo a birnin Khan Yunus da hakan ya tilastawa farar hula da suka rasa matsuguni sake tserewa.

Kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa mayakanta na ci gaba da gwabza ƙazamin faɗa da sojojin da suka mamaye dukkan yankuna a kokarinsu na kutsawa cikin zirin Gaza, sun kuma yi ikirarin sun lalata motocin sojan Isra’ila biyu a Khan Yunis da Beit Lahia.

Wata sanarwa ta faifan bidiyo ta nuno Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cikin sojoji y ana cewa dakarun kasar na kutsawa gidan shugaban Hamas Yahya Sinwar a Gaza, inda suke tsammanin ya na wani ginin karkashin kasa a yankin Khan Yunis.

Sai dai kungiyoyin agaji sun yi gargadin yaduwar yaƙin da Isra’ila ke yi a kudancin Zirin Gaza zai sa farar hula da suka tsere daga arewacin kasar kara shiga halin ha’u’la’i da rashin zaɓin inda za su.