Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnan Kano ya amince da wasu sababbin nade-nade

Gwamnan Kano ya amince da wasu sababbin nade-nade

Date:

A halin da ake ciki kuma Gwamnan Kanon ya amince da wasu sababbin nade-nade ciki har da daukaka matsayin Sunusi Bature Dawakin Tofa daga babban sakataren labarai zuwa babban darakta.

Wata sanarwar daraktan wayar da kan al’umma na gidan gwamnati, Aliyu Yusuf ta ce karin matsayin ya fara aiki nan take.

Sanarwar ta kuma ruwaito cewa gwamnan ya amince da wasu nade-nade a bangarori da dama na gwamnatin jihar Kano da suka hada da Dr Dahiru Saleh a matsayin babban sakataren hukumar kula da makarantun kimiyya da fasaha, da Rabi’u Saleh Gwarzo da a ka nada babban kwamishinan hukumar ilmin baidaya, sai Abubakar Adamu Rano da aka nada sabon mataimakin shugaban gidan radio Kano, sai Hajiya Hauwa Isa Ibrahim da aka ba mataimakiyar babban daraktan gidan talabijin na ARTV, da ma wasu da dama.

Gwamnan ya kuma amince da nadin karin wasu mutane goma sha uku a matsayin masu bashi shawarar musamman a bangarorin tafiyar da gwamnatin daban-daban.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...