Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dattawa ta fitar da bayanin kasafin kudin da shugaba Tinubu ya...

Majalisar dattawa ta fitar da bayanin kasafin kudin da shugaba Tinubu ya gabatar

Date:

Majalisar dattawa ta kasar nan ta fitar da bayani kan kasafin kudin da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar mata a ranar laraba da ta gabata.

Wannan ya biyo bayan rahotanni da suka ce fankon kasafin kudi shugaba Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar.

Wani dan mahalisar tarayya Hon Yusuf Shitu Galambi ya tabbatarwa da kafar BBC cewa babu komai a cikin akwatin kasafin kudin da shugaban kasa Tinubu ya ajiye a gaban zauren majalisar.

To sai dai daga karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kudaden da aka ware wa ma’aikatu da sauran bangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

Tuni ma dai majalisar tayiwa kasafin shekarar 2024 karatu na 2, wanda yawansa ya kai triliyan 27, da miliyan dubu 500.

Bangaran tsaro ne ya samu kudi mafi yawa wato kaso 12 cikin 100, da ya haura Tiriliyan 3 da miliyan dubu 200 sai kuma bangaran ilmi da ya samu kaso kusan kaso 8 cikin 100 da adadin kudin yah aura triliyan 2 da miliyan dubu 200.

Bangaran lafiya ya smau kaso 5 cikin 100, da yawan kudin ya kai tiriliyan 1 da miliyan dubu 400. Sai kuma manyan ayyuka da ya samu kaso 5 cikin 100 da yawan kudin ya kai kusan tiriliyan 1 da miliyan dubu 320.

Latest stories

Related stories