Jam’iyyar APC ta daukaka kara zuwa kotun ƙoli domin a tabbatar mata da Gawuna a matsayin Gwamnan Kano.

APC ta daukaka kara akan nasarar da ta samu a kotun daukaka kara domin kotun koli ta kara tabbatar mata da nasarar da alkalan kotun daukara suka tabbatar mata.

Hakan ya biyo bayan matsalar rubutu da aka samu a cikin rubutaccen hukunci da kotun ta fitar.

A hukuncin da kotun ta sanar, ta soke zaben Abba Kabir na NNPP tare da tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Sai dai bayan fitar da takardun hukuncin, sai wani bangare na takardun ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf na NNPP ne ya yi nasara a hukuncin, yayin da wani bangaren ke nuna cewa Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara.

Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce mai tarin yawa, tare da jefa shakku a zukatan jama’a.

To sai dai cikin wata sanarwar da magatakardar kotun ɗaukaka ƙarar, Umar Mohammed Bangari, ya fitar, ya ce ya amince da kuskure a cikin takardun hukuncin da kotun ta fitar.

Tuni dai majalisar shari’ar ta kasa ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafen da suka shafi shari’ar, inda ta alƙawarta duba lamarin kamar yadda dokoki suka tanada.