Jam’iyyar NNPP ta nemi kasar Amurka da kungiyar tarayyar Turai da ta Afrika, su tsoma baki a cikin shari’ar zaben gwamnan jihar Kano, ta na mai bayyana cewa ana kokarin murde nasarar Abba Kabir Yusuf.

Yayin wata zanga-zanga a ofisoshin jakadancinsu da ke Abuja, shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Kawu Ali, ya ce kwafin kundin shari’ar kotun daukaka kara, ya nuna cewa Abba ne ya yi nasara a zaben gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris.

Ya ce zanga-zangar a ofisoshin jakadancin kira ne a gare su, da su sanya baki domin tabbatar da tsarin dimokradiyya.

Masu zargar-zangar sun kara yin tattaki zuwa ofisoshin jakadancin majalisar dinkin duniya da na ECOWAS da ke Abuja, tare da yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su sanya baki domin ganin an yi adalci a shari’ar.