Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Date:

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta dakatar da mai horas da yan wasanta, Abdu Maikaba nan take.

Hakan ya biyo bayan kafa wani kwamiti da zai binciki aikin kocin tare da bayar da shawarar daukar mataki na gaba.

Idan dai za a iya tunawa, Abdu Maikaba yayi wasu kalamai na rashin jin dadi dadi a kwanakin baya game da gudanarwar kungiyar yayin wani taro da magoya bayan Kano Pillars din suka shirya a nan Kano.

Matakin dakatar da shi ya zo ne kwanaki bayan da tsohon dan wasan Enugu Rangers din ya bayyana cewa bai samu ingantaccen yanayin aiki ba tun lokacin da ya karbi ragamar shugabanci a farkon kakar bana.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...