Saurari premier Radio
24.7 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiCBN ya bayar da wa'adin 7 ga Yuli, 2024 ga masu sana'ar...

CBN ya bayar da wa’adin 7 ga Yuli, 2024 ga masu sana’ar POS da su kammala rajistar CAC.

Date:

Babban bankin kasa CBN, ya bayar da wa’adin ranar 7 ga Yuli, 2024 ga masu sana’ar hada hadar kudi ta POS, akan su tabbatar da sun kammala rajista da Hukumar rajistar kamfanoni ta kasar wato CAC.

Bayanin hakan ya biyo bayan wata ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasar nan, da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji wadda ta gudana a Abuja yau Talata.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban na hukumar ta CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin kasa.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta kuma ta kara da cewa An ɗauki matakin ne domin kare masu mu’amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi tare kuma da ƙarfafa tattalin arziƙin kasa.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...