Saurari premier Radio
27.2 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniManchester City na jimamin ficewa daga gasar Carabao Cup

Manchester City na jimamin ficewa daga gasar Carabao Cup

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta fice daga gasar cin kofin Carabao Cup, bayan rashin nasara a hannun Southampton da ci 2-0.

 

Wasan dai ya gudana a ranar Laraba a filin wasa na St. Mary’s da ke Ingila.

 

Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Southampton’s Sekou Mara da Moussa Djenepo ne suka zura kwallaye biyun a minti na 23rd da 28.

 

Yanzu haka dai kungiyar kwallon kafa ta Southampton ta kai wasan kusa da karshe a gasar ta Carabao Cup.

 

Inda Southampton zata kece raini da Newcastle, sai kuma Nottingham Forest da Manchester United.

 

Wasannin kusa da karshen za gayen farko zasu gudana A ranar 23 ga Janairun da muke ciki.

 

Sai kuma wasannin za gaye na biyu na gasar ta Carabao Cup za su gudana a ranar 30 ga watan na Janairun..

 

Haka kuma wasan karshe zai gudana a katafaren filin wasa na Wembley a ranar Lahadi wato 26 ga Fabrairu Mai kamawa .

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...