Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniMane ka iya buga wasan Bayern Munich da PSG a Champions league-...

Mane ka iya buga wasan Bayern Munich da PSG a Champions league- Nagelsmann

Date:

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Julian Nagelsmann, na fatan Sadio Mane zai buga wasan farko da Bayern Munich za tayi a gasar cin kofin zakarun turai da kungiyar kwallon kafa ta PSG.

 

Mane wanda ya ji rauni tin a watan Nuwamba, da hakan ya sa bai buga gasar cin kofin duniya da ta gudana a Qatar ba.

 

Dan kasar Senegal Mane, wanda ya koma Munich da ke buga Bundesliga daga Liverpool a watan Yunin bara ya samu rauni da ya sha fama da jinya.

 

Nagelsmann ya ce ba shi da tabbas ko Mane zai buga wasan da za suyi da PSG a Parc des Princes a watan Fabrairu a ranar 14 ga wata.

 

Sai da ya ce yana fatan Dan wasan Mai shekara 30 ya murmure kafin wasan, wanda hakan ka iya bashi damar buga wasa na biyu da zakarun gasar Ligue 1 a wasa na biyu da zasu buga a Allianz Arena a ranar 8 ga Maris.

 

Yanzu haka dai Bayern Munich na shirin buga wasan sada zumunta da Salzburg a ranar Juma’a, kana Kuma ta buga wasan gasar Bundesliga da RB Leipzig a Juma’ar makon gobe.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...