Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniGoyan bayan Obi da Obasanjo ya yi babban Kuskure ne–Sule Lamido

Goyan bayan Obi da Obasanjo ya yi babban Kuskure ne–Sule Lamido

Date:

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce goyan baya da Olusegun Obasanjo, ya yi ga Peter Obi babban kuskure matuka.

 

Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin tsohon mataimakin gwamnan Jigawa Ahmad Mahmoud, zuwa jam’iyyar PDP.

 

Peter Obi wanda shi ne Dan takarar Shugaban kasa na jami’iyyar LP a zaben 2023, a makon da ya gabata aka jiwo Obasanjo ya goyi bayan takarar tashi.

 

Sai dai Sule Lamido ya ce Obasanjo ya kasa fahimtar cewa PDP ce ta mayar da shi duk abin da ya zama a yanzu.

 

“Obasanjo ya yi magana ne a matsayinsa na tsohon Shugaban Kasa, kuma PDP ce ta mayar da shi duk abin da yake takama da shi a yau”, a cewar Sule Lamido. A cewar Sule Lamido.

 

“Shakka babu na yarda Obasanjo maigidana ne, amma kuma shi mutum ne, zai iya yin kuskure, kuma yanzu ma ya tafka shi ta hanyar goyon bayan wani daban”,

 

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Sule Lamido ya kara da cewa Shi da kansa ya San yana girmama Obasonjo, amma dole su tsaya kan akidun jam’iyyarsu ta PDP.

 

Ya ci gaba da cewa tunaninsa ya bashi cewa goyon bayan Peter Obi fiye da Atiku ko Tinubu a matsayin nagartattun hakan zai kawowa kasar dauki.

 

Sai dai yace sam Peter Obi bai fi ragowar Yan takarar  nagarta .

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...