Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano zata tantance sabon kwamishinan al'amuran addinai bayan korar Baba...

Majalisar dokokin Kano zata tantance sabon kwamishinan al’amuran addinai bayan korar Baba Impossible.

Date:

Majalisar dokokin Kano ta karbi sunan Muhammad Nazifi Bichi, domin tantance shi a matsayin sabon kwamishina da zai maye gurbin tsohon kwamishinan ma’aikatar al’amuran addinai na jihar nan Tahar Baba Impossible.

 

Gwamnatin Kano ta sharara karya kan korata-Baba Impossible

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ne ya aike da sunan sabon kwamishinan a zaman majalisar na Litinin din nan.

Wannan na zuwa ne biyo bayan korar tsohon kwamishinan da gwamnatin Kano tayi a shekarar data gabata.

Majalisar ta bukaci Muhammad Nazifi Bichi, da ya bayyana a gaban majalisa a gobe Talata domin tantance shi.

 

A dai zaman na yau majalisar ta amince da karatu na biyu na gyaran dokar fansho data hukumar majalisar dokoki da kuma dokar sufuri ta 1963.

 

Majalisar dokokin ta kuma karbi sunayen Baba Hamidu Yalwa da Bello Abdullahi daga hukumar ilimin bai daya Subeb don tatance su a matsayin sakatarorin ilimi na kananan hukumomin Bebeji da Dala.

Majalisar ta kuma dage zamanta zuwa gobe Talata.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...