Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu Ne Ya Dauki Nauyin Jifan Da Aka Yiwa Buhari A Kano...

Tinubu Ne Ya Dauki Nauyin Jifan Da Aka Yiwa Buhari A Kano – PDP

Date:

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Allah wadai da jifan da aka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano jiya Litinin.

 

Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a daren jiya, tace dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ne ya shirya jifan da aka yiwa Buharin, domin haifar da rikici a Najeriya da zai kawo tsaiko a zaben da ke tafe, saboda ya lura ba zai yi nasara ba.

 

PDP tace Tinubu da Ganduje sun shirya cin mutuncin Buhari shi yasa aka yi kokarin hanashi ziyartar Kano tun da farko.

 

“Ya kamata a lura cewa dan takarar shugaban kasa na APC ya dade yana fito na fito da shugaba Buhari tun lokacin da Buhari yayi kira ga yan Najeriya su zabi wanda suka ga dama a zaben 2023.”

 

PDPn ta kuma yi tir da batagarin da suka jefi shugaba Buharin a Kano wanda tace Bola Tinubu ne ya dauki nauyinsu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...