Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta sharara karya kan korata-Baba Impossible

Gwamnatin Kano ta sharara karya kan korata-Baba Impossible

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Tshohon kwamishinan al’amuran addinai na jihar Kano Muhammad Tahar Adam Baba Impossible ya ce ya yi mamakin karyar da gwamnantin Kano ta kitsa kan batun korarsa.

 

Baba Impossible ya yi wannan jawabinne ta cikin wani sakon murya da ya aikewa Freedom Radio da yammacin yau.

 

Ya ce tun ranar Juma’ar da ta gabata ya rubuta takardar barin aiki ya kuma kaiwa sakataren gwamnatin Kano da Shugaban ma’aikata aka kuma karba aka saka masa hannu.

Sai dai ya ce ga mamakinsa sai gani ya yi a kafafen yada labarai cewa gwamnatin Kano ta koreshi.

 

“Ni a zatona gwamnati, cikakkiyar gwamnati, bai kamata ta yi karya ba.

 

” Dan wannan itace karya hakika mai gishiri, mutum ya je ya kai takarda a karba, ayi masa signing, sakataren gwamnati da Head of Service, kuma wani ya fito ya ce an koreka to ta ina aka koreka?

 

” Bayan an korenin ne aka karbi takardar tawa? Ko Kuma bayan na mika katardar aka koreni? A cewar Baba Impossible.

 

Ya ce sun dai bar wannan zance a haka amma idan gwamnati ta ci gaba da magana a kai to shi ma zai dora da zancensa.

 

Idan za a iya tunawa da safiyar ranar Asabar ne gwamnatin Kano ta sanar da korar Kwamishinan daga aiki, cikin wata sanarwa da ta fitar.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...