Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan Shi'a sun gudanar da zanga-zangar adawa da umarnin kashe Abduljabbar Kabara

‘Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zangar adawa da umarnin kashe Abduljabbar Kabara

Date:

Wasu yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a babban masallacin kasa da ke Abuja domin nuna adawa da hukuncin da aka zartarwarwa Abduljabbar Nasir Kabara.

An dai gudanar da zanga-zangar ne a harabar babban masallacin juma’a da ke Abuja, a jiya Juma’a.

Yan Shi’ar sun kuma nemi gwamnatin Kano ta gaggauta sakin Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara tare da janye hukuncin da kotun Shari’ar Musulunci ta zartar a kan sa.

Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye masu hotunan Sheikh Abduljabbar Kabara, da ke nuna anyi masa rashin adalci.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan nan na Disamba ne wata babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotun dai ta ce ta sameshi da  laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam

Latest stories

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories