Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2023 fiye da...

Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin shekarar 2023 fiye da miliyan dubu 268

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin jihar nan na shekarar 2023 da ya zarta naira biliyan dari biyu da sittin da takwas.

 

Majalisar ta amince da kasafin ne a zaman ta na Alhamis din nan karkashin shugaban ta Hamisu Ibrahim Chidari.

Ganduje zai gabatar da kasafin kudin badi ranar Juma’a

Kasafin kudin na badi dai shine naira biliyan dari biyu da sittin da takwas da miliyan dari da casa’in da bakwai da dari bakwai da talatin da daya.

Kudirin gyaran dokar fansho ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano

A watan Nuwambar da ya gabata ne Gwamna Ganduje, ya gabatarwa da majalisar kasafin kudi na naira biliyan dari biyu da arba’in da biyar da miliyan talatin da daya da dari biyar da goma sha shida da naira casa’in da hudu da kwabo takwas.

 

Saidai an samu kari kan abinda gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatarwa da majalisar da naira biliyan ashirin da uku da miliyan dari da sittin da shida da dari biyu da sha hudu da naira dari tara da biyar da kwabo casa’in da biyu.

 

Kafin amincewa da kasafin ma’aikatu da hukumomi na jihar nan dai sun bayyana a gaban majalisar inda suka kare kasafin kudin su.

 

Latest stories

Related stories