Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar 'yan fansho: Kuyi biyayya a dauki hoton 'yan yatsun ku 'yan...

Kungiyar ‘yan fansho: Kuyi biyayya a dauki hoton ‘yan yatsun ku ‘yan fansho

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Kungiyar ‘yan fansho ta kasa reshen jihar Kano (Nigerian Union of Pensioners) tayi kira ga ‘yan fansho da suyi biyayya ga tsarin da gwamnati ta fito dashi na tantance su ta hanyar daukar hoton ‘yan yatsun su.

 

Mataimakin shugaban kungiyar na Kano Shu’aibu Musa Jibril, ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Larabar nan.

 

Ya ce shugabancin kungiyar ‘yan fansho zai tabbatar da cewa anyi tantancewar cikin sauki ba tare da kowane dan fansho ya wahala ba.

 

Kudirin gyaran dokar fansho ya tsallake karatun farko a majalisar dokokin Kano

 

Ya ce za a fara tantancewar ne da ma’aikatan gwamnati sannan daga bisani ayi na ‘yan fansho.

Jibril, ya kara da cewa daukar hoton ‘yan yatsun shine zai tabbatar da cewa mutum yana raye.

 

Ya kuma ce wannan ba sabon abu bane domin kuwa a baya an taba yin irin wannan tantancewa.

 

Ganduje zai nada sabon kwamishina a hukumar fansho

 

Ya ce a yanzu an samu cigaba a yadda ake tantance ‘yan fansho idan aka kwatanta da baya.

 

 

Ya ce an tanadi guraren a kananan hukumomi wanda kowane dan fansho zaije domin a dauki hoton ‘yan ya tsunsa.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...