Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGanduje zai nada sabon kwamishina a hukumar fansho

Ganduje zai nada sabon kwamishina a hukumar fansho

Date:

Gwamnatin jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike da sunan Usman Waziri Kiru, gaban majalisar dokokin Kano, don tantamcewa tare da amincewa a nada shi kwamishina na daya a hukumar Fansho ta jihar nan a Talatar nan.

 

Bayan da shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta takardar  majalisar ta mikawa kwamitin ta na Fansho karkashin dan majalisa Ayuba Labaran Durum mai Wakiltar Kabo don tantance shi tare da gabatar da rahotan sa a ranar Laraba.

 

Nadin Usman Waziri, ya biyo bayan ajiye aiki da Bello Maifada Kibiya yayi.

 

Haka zalika majalisar ta karbi  wasika daga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje dake bukatar amincewa da nada Rabi’u Yusuf Gezawa, a matsayin kwamishina na dindin din da Muhammad Bashir a matsayin kwamishina mai takaitaccen zango a hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci ta jihar nan.

 

Wakilin mu Aminu Abdullahi Ibrahim, Ya ruwaito cewa majalisar ta mikawa kwamitin ta dake lura da hukumar karkashin dan majalisa mai wakiltar Kura da Garin Malam, Hayatu Musa Dorawar Sallau, don gabatar da rahoton sa nan da mako guda.

Latest stories

Related stories