33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiBuhari zai gabatarwa da majalisun kasa kasafin kudin 2023

Buhari zai gabatarwa da majalisun kasa kasafin kudin 2023

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa da majalisun kasa kasafin kudin shekarar 2023 wanda ya kai naira tiriliyan 19.76 a ranar Juma’a mai zuwa 4 ga watan Oktoba da muke ciki.
Buhari dai zai gabatar da kasafin kudin ne da misalin karfe 10:00 na safe a babban zauren majalisun kasa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar gabatar da kasafin kudin da shugaban kasa Buhari ya aikowa da majalisar a yau Talata.
Wannan dai shine kasafin kudi na karshe da shugaba Buhari zai gabatar kasancewar wa’adin mulkin sa zai kare a ranar 29 ga watan Mayun shekara mai kamawa.

Latest stories