Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKisan Ummita: Kotu ta dage shari'ar dan China

Kisan Ummita: Kotu ta dage shari’ar dan China

Date:

Babbar Kotun jihar Kano me lamba 17 ta dage sauraron karar da aka shigar da wani kasar China Mr. Geng Quangrong wanda  ake zargi da kashe budurwarsa mai suna Ummukulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita.

An dage shari’ar ne bayan lauyan wanda ake kara Barista Muhammad Dan’azumi ya roke a dage zaman sakamakon wanda ake kara baya fahimtar turanci, inda ya bukaci a samo tafinta.

Alkalin kotun ya amince da bukatar, tare da dage shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Octoba.

A ranar 16 ga watan Satumba ne Mr. Geng ya hallaka budurwar sa Ummita a gidansu dake unguwar Jambulo a jihar Kano.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...