Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSon zuciya ne yasa ake nuna banbanci tsakanin masu degree da HND-Masani

Son zuciya ne yasa ake nuna banbanci tsakanin masu degree da HND-Masani

Date:

Wani babban ma’aikaci daga kungiyar manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya, kwamared Abubakar Tanimu Dorayi, ya bayyana son zuciya a matsayin abun da ya sa ake nuna bambanci tsakanin masu shaidar karatun babbar diploma ta HND da degree a daukar aiki.

 

Tsokacinsa ya biyo bayan wani rahoto da ya bayyana yadda ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya fitar da wata wasika da ke nuna yadda har yanzu gwamnati ke daukar wadanda suka kammala karatun digiri sama da takwarorinsu masu HND Diploma.

 

Wakisar dauke da kwanan watan Agustan bana, ta bayyana a fili cewa, masu takardar shaidar Diploma ta HND ba za su iya zama mataimakan darakta ko darakta ba, ko ma babban sakatare, duk da dokar da majalisun tarayya sukayi na kawar da nuna bambanci tsakaninsu da masu shaidar digiri.

 

Sai dai kwamared Tanimu Dorayi, ya ce duk da bambancin da ake nunawa masu HNDn sun fi nuna kwarewa a aiki.

 

Ranar 8 ga watan Yunin bara ne majalisar dattawa ta zartar da kudirin soke sauye-sauyen da ake samu tsakanin HND da Digiri, domin kawo karshen wariyar da ke tsakani.

Latest stories

Related stories