Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZamu baiwa hukumar kidaya dukkanin goyon baya-Gawuna

Zamu baiwa hukumar kidaya dukkanin goyon baya-Gawuna

Date:

Gwamnatin Kano ta yi alkawarin bayar da cikakkiyar gudummuwa ga hukumar kidaya ya yin da ake shirin fara kidayar al’umma a watan Aprilun badi.

Mataimakin gwamana, Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka, yayin wani taron wayar da kai na masu ruwa da tsaki kan harkar kidayar da z ‘a gudanar, da hukumar kidaya ta kasa da hadin gwiwar gwamnatin Kano suka shirya.

Gawuna wanda ya wakilci Gwamna Abdullahi Ganduje a taron, ya ce wajibi ne al’ummar Kano su fito, su kuma bayar da dukkan goyon baya ga kidayar, domin gwamnati ta san addadin al’ummarta, yadda za ta samu damar ayyukan more rayuwa.

Shi ma shugaban ofishin hukumar kidayar a nan Kano, Dr Ismail Lawan Sulaiman, ya ce za a yi kidayar ne da na’urorin zamani domin tabbatar da ganin komai ya tafi yadda ake so.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories