25.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamantin Kano ta samar da sabbin kotunan musulunci 3

Gwamantin Kano ta samar da sabbin kotunan musulunci 3

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamantin Kano ta samar da sabbin kotunan musulunci uku a wani bangare na rage cunkosu a kotunan Kano.

 

Wannan na zuwa ne bayan cece-kucen da aka samu kwanakin baya game da sauyawa wasu kotunan addinin musulunci matsuguni.

 

Kakakin manyan kotunan shari’ar musulunci na Kano, Muzammil Ado Fagge, ne ya sanar da samar da sabbin kotunan ranar Litinin.

 

Ya ce samar da karin, da ma wadanda ake da su a baya za su rage cunkuson da ake samu, tare da taimakawa gudanar da shari’a cikin sauri.

 

Muzammil Fagge, ya kuma yaba jajircewar Alkalin-Alkalai, Tijjani Yusuf Yakasai, da magatakardar kotuna, Barista Abubakar Haruna Khalil, wajen tabbatar da samar da wadannan sababbin kotuna.

 

Kwanakin baya dai an zargi gwamnatin Kano da laifin sayar da harabar wasu kotunan shari’ar musulunci al’amarin da Kwamishinan sharia, Musa Abdullahi Lawan ya musanta.

Latest stories