Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar masu sana’ar gawayi ta bukaci a daina sare bishiyu

Kungiyar masu sana’ar gawayi ta bukaci a daina sare bishiyu

Date:

Kungiyar masu sana’ar gawayi da safararsa zuwa ketare, wato ta yi kira ga masu samar da gawayi su rage sare itatuwa ba tare da maye gurbinsu ba.

 

Wannan na zuwa ne a kokarin da kungiyar ke yi na magance kwararowar hamada a fadin kasar nan

 

Shugaban kungiyar, Tunde Ede, ne ya yi wannan kira a Minna babban birnin Jihar Neja.

 

Ya ce akwai bukatar yawaita shuka sabbin bishiyoyin da za su maye gurbin wadanda ake sarewa domin samar da gawayin da ake girki da shi.

 

Sai dai a tattaunawarsa da Premier Radio, Suleiman Gidado Isma’il, wani mai rajin kare muhalli, ya ce in-so- samu-ne a daina sare itatuwa baki daya.

 

A cewarsa akwai hanyoyin samar da makamashi kamar ta hanyar amfani da ragowar kayan miya, da wasu dabaru domin samar da tsaftataccen gas na makamashin girki.

 

Suleiman Gidado, ya kuma kara da cewa, hanyoyin samar da irin wannan makamashin gas masu tsafta basu da wahala sosai matukar aka samu tallafin da ya dace.

 

Ya ce duk da cewa yanzu haka babu wata kungiya dake samar da irin wannan a Kano, sun taba horar da matasa yadda za su samar da makamashin amma basu fitar da batun ta fuskar kasuwanci ba.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...