Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiFyade:Yadda Baba Idi ya hallaka 'yar shekara 3 a Kano

Fyade:Yadda Baba Idi ya hallaka ‘yar shekara 3 a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Wani mutum dan shekaru 40 mai suna Baba Idi ya hallaka wata karamar yarinya mai suna Siyama Muhammad mai shekaru uku jim kadan bayan ya yi mata Fyade.

 

Al’amarin ya faru cikin makon jiya a Unguwar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa a nan Kano.

 

Rahotanni sun ce, kwanaki shida da suka gabata, aka zargi Baba Idi da daukar Siyama zuwa dakinshi domin  ya bata Alewa.

 

Sai dai ya bige da yin lalata da ita kuma ya tsoratar da ita cewar indai ta fadawa babanta sai ya kasheta da Almakashi.

 

Haka kuma ya kara tsoratar da ita cewar inda ta fada sai ya hadata da magen gidansu ta cinyeta.

 

Yarinyar dai ta kwatanta yadda ya dora mata almakashi a wuya, ya ce, sai ya yankata da shi idan ta fada.

 

Bayan siyama ta shiga gida ne ana kokarin yi mata wanka iyanyenta suka ga jini na fita daga jikinta, inda mahaifyarta ta tambayenta abinda ya sameta.

 

Sai ta ce “Baba Idi ne yake min wani abu, yauma ya ciremin wando ya yi min ya bani alawa.

 

“Ya ce  idan na fadawa Abbana zai kasheni, Umma don Allah kar ki fadawa Abba”. A cewar yarinyar.

 

Daga nan aka dauketa aka kaita asibiti, inda likitoci suka tabbatar da fyade aka yi mata kuma suka fadi hanyoyin da za a bi a kula da lafiyarta.

 

Sai dai bayan jami’an tsaro sun kamashi ne iyayen suka je bada bayani inda yarinyar ya gashi ta kuma rude ta fadi aka yi asibiti da ita.

 

Tun da ta ganshi ta ke fadin “Kasheni zai yi har kasha gari da ta rasu ta na ta maimaita maganar.

 

Tuni dai jami’an tsaro suka ci gaba da bincike kan al’amarin.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories