24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin Kaduna ta umarci jami’an tsaro su kamo wadanda suka kashe Fulani...

Gwamnatin Kaduna ta umarci jami’an tsaro su kamo wadanda suka kashe Fulani 2

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin Jihar Kaduna ta umarci jami’an tsaro su kamo wadanda su ka kashe wasu Fulani biyu matasa da aka zarga da hannu a harkar satar mutane.

 

Rahotanni dai sun ce wasu fusatattun matasa ne suka bankawa fulanin wuta bayan sunyi zargin yan ta’adda ne a garin Birnin Gwari.

 

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan  ne ya sabar da hakan ga manema labarai.

 

Ya ce gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da daukar doka a hannu da matasan suka yi.

 

Ko da yake jami’an tsaro sun kai musu dauki amma jama’a suka kwace su daga hannun jami’an tsaron suka kona.

Latest stories