Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayya ta gargadi ASUU kan kin bin umarnin Kotu

Gwamnatin tarayya ta gargadi ASUU kan kin bin umarnin Kotu

Date:

Gwamnatin tarayya ta gargadi kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU bisa kin bin umarnin kotun Ma’aikata na janye yajin aikin da take yi.

 

Ministan Kwadago da Nagartar Aiki Dakta Chris Ngige ne ya yi gargadin cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran ma’aikatar Mista Olajide Oshundun a karshen mako.

 

“Kungiyar ba ta yi dattako ba kuma tana yaudarar mambobinta da sauran jama’a, maimakon ASUU ta shigar da bukatar neman izinin daukaka kara kawai tayi gaban kanta.

 

Ministan ya shawarci malaman da ke yajin aikin da su daina daukar doka a hannunsu ta hanyar umurtar mambobinta da su ci gaba da yajin aikin na watanni 8.

 

A cewar sa, hakan ya sabawa umarnin shiga tsakanin da hukumar ta NICN wanda ya hana kungiyar daukar kowamne irin mataki.

 

Ya zargi shugabannin kungiyar da yin gaban-kansu tareda yaudarar mambobinta.

 

Ngige ya nanata kiran gwamnati ga kungiyar da ta mutunta umarnin kotu tare da komawa bakin aiki, yayin da ake tattaunawa kan sauran batutuwan da ake takaddama a kan su.

 

Sanarwar ta kuma musanta rahotannin da ke cewa ministan ana tsaka da taro ya fice daga taron majalisar wakilai da kungiyar ASUU ta gudanar a ranar 29 ga watan Satumba.

 

Sanarwar ta ce ministan ya bar gurin taron ne domin halartar wasu muhimman batutuwa bisa ga izinin shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila bayan ya gabatar da jawabinsa.

 

Sanarwar ta kuma ce a wancan taro, Ngige ya yi jawabai da maganganu kan manyan batutuwa biyu da har yanzu ASUU ke yajin aikin akan su.

 

“Akan sake tattaunawa kan batun albashi da albashin malamai, ina tausayawa ASUU kamar sauran ma’aikatan Najeriya”. Inji Ngige.

 

Ngige ya kuma bayyana cewa lokacin da suka tattauna batun tsarin biyan albashin kudi – UTAS – ya jawo hankalin Shugaban kasa da yabasu dama ayiwa dandamalin gwaji bisa tsarin zartarwa na 3 da 4”.

 

“Idan tsarin ya kyautatu se a ɗauke shi ayi amfani da shi aduk fadin ƙasa, amma kuma babu cikakkun kayan aikin nayin gwajin. To ya kuke so a yi?

 

“Gwajin da akayi guda uku na IPPIS, UTAS, UPPPS sun gaza tsallake matakan gwaji, to aganin ku zamuyi aiki da abin da ya gaza tsallake matakin gwaji ne?. Don haka, duk yadda nake son ASUU, ba zan goyi bayan wani abu da ya gaza tsallake matakan gwaji ba.’’

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...