Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNDLEA ta kama tramadol miliyan 13 a Lagos

NDLEA ta kama tramadol miliyan 13 a Lagos

Date:

Hukumar  NDLEA ta kai samame wani gidan alfarma a Unguwar Lekki a Legas inda ta ce ta gano miyagun ƙwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol guda miliyan 13 a gidan .

Ya bayyana cewa duka ƙwayoyin suna da nauyin miligram 225.

Mista Femi ya bayyana cewa gidan babu wani bil adama da ke zaune a ciki, sai dai waɗannan ƙwayoyi da aka ajiye a ciki.

Tun da farko dai hukumar NDLEA ta ce ta samu bayanan sirri ne a ranar 30 ga watan Satumba inda ta kai samame gidan.

Bayan gudanar da bincike, sai aka gano kwalaye 443 na ƙwayar Tramadol ɗauke da ƙwayoyi 13,451,466 inda hukumar ta ce wasu kwalayen ma sun ƙone sakamakon gobarar da ta tashi a gidan a ranar da aka kai samamen.

Hukumar ta ce dama wanda ake zargin mai suna Ugochukwu asalin ɗan Ƙaramar Hukumar Ihiala ne da ke Jihar Anambra kuma dama yana daga cikin waɗanda take sa ido a kansu.

Tuni dai aka kama wanda ake zargin kuma a halin yanzu yana hannun hukumar ta NDLEA.

A ƴan kwanakin nan dai hukumar ta NDLEA na wawan kamu inda ko a kwanakin baya sai da ta kama hodar ibilis ta biliyoyin naira da kuma dubban kwalaben A-Kurkura da tabar wiwi a samame daban-daban da ta kai a fadin Najeriya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...