Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMagoya bayan Peter Obi sun bijirewa umarnin Kotu

Magoya bayan Peter Obi sun bijirewa umarnin Kotu

Date:

Magoya bayan Peter Obi sun bijirewa umarnin kotu yayin da suka yi gangamin magoya baya a kofar Lekki Toll Gate dake birnin Legas a ranar Asabar.

 

Duk da ‘yan sandan da aka baza a kan titi, magoya bayan Peter Obi sun haifar da cunkoson ababen hawa da safe yayin da motoci masu zaman kansu da direbobin bas suka nemi wasu hanyoyin da za su bi.

 

Wani direban da ya zanta da jaridar Punch ya bayyana yanda lamarin ya auku “Mutanen Peter Obi Sun kashe hanya, na dad’e a cikin cunkoso kafin in samu hanyar wucewa amman daga baya jami’an tsaro sun zo wajen domin tabbatar da masu gangamin sunbi umarnin kotu”.

 

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya babbar kotun jihar ta yanke hukuncin dakatar da magoya bayan jam’iyyar labour party daga gabatar da gangamin da suka shirya gabatarwa tun da fari.

 

Kakakin ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce an baza jami’an yan Sanda a wajen taron domin tabbatar da komai ya tafi bisa tsarin doka.

 

Inda ya kara da cewar rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tura ‘yan sandan Rapid Response Squad (RRS) zuwa kofar shiga Lekki domin dakatar da gangamin da magoya bayan Peter Obi sukayi.

 

Latest stories

Related stories