Saurari premier Radio
34.3 C
Kano
Monday, September 25, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiIndependence: Matasa ku kauracewa bangar siyasa-Sarkin Kano

Independence: Matasa ku kauracewa bangar siyasa-Sarkin Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya roki matasa da su kaucewa siyasar daba da ta uban gida yayin zabe mai zuwa.

 

Sarkin ya yi Wanann rokon ranar Asabar yayin da ya jagoranci yiwa kasa addu’o’i a Wani bangare na bikin zagayowar ranar samun yancin kai.

 

Ya kuma ja hankalin yan siyasa da su rika yin kalamai masu inganci a cikin al’umma.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ya shirya taron addu’ar ne domin yiwa kasa addu’a da kuma zabuka da suke tunkararmu a shekara 2023.

 

Mai martaba sarkin ya yi kira ga Matasa su gujewa dukkan abinda zai kawo fitina a lokutan yakin neman zabe.

 

Sarkin ya bukaci Al’umma su zama masu Ladabi da biyayya da tausasa harshinansu.

 

Yayi fatan dukkan yan siyasa za su karbi shawarwari da Malamai suke bayarwa na suyi yakin neman zabe cikin nutsuwa ba tareda wani tashin hankali ba.

 

Sarkin ya ce shirya adduoin yazo dai dai da lokacin da ake bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun yancin kai.

Latest stories

Related stories